Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Karin ‘yan Nijeriya  129 sun dawo gida  daga Sudan

Published

on

Karin ‘yan Nijeriya 129 sun dawo gida daga kasar Sudan bayan da suka tsere wa yakin da ake gwabzawa a Khartoum babban birnin kasar Sudan.

Gwamnatin tarayya dai na ci gaba da dawo da  ‘yan Najeriya da suka makale a kasar da ke Arewacin Afirka.

Gidan Talabijin na Channels ya rawaito cewa mutanen sun isa Najeriya ne jiya Litinin da karfe tara da minti goma sha biyar na dare cikin jirgin Tarco inda suka sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.

Mutanen sun samu tarba daga jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa NEMA da na hukumar da ke kula da ‘yan Najeriya mazauna ketare da na ma’aikatar jin kai da ma’aikatar harkokin waje sai kuma hukumar kula da shige da fice ta kasa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!