Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamna Abubakar Sani Bello ya rantsar da dan takarar NNPP

Published

on

Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya rantsar da dan takarar jam’iyyar NNPP Abdul-Alim Abubakar a matsayin sabon shugaban karamar hukumar Gurara.

Rantsar da Abubakar ya biyo bayan umarnin da wata babbar kotun jihar, wacce ta soke zaben dan takarar jam’iyyar APC Yusuf Walid.

A baya dai an ayyana Walid a matsayin wanda ya lashe zaben kansiloli da aka yi ranar 10 ga Nuwamba 2022.

Sai dai nasarar tasa ta fuskanci kalubale daga wani dan jam’iyyar Saudaki Abubakar wanda ya soki zaben shugaban da kotu ta tsige a matsayin dan takarar da aka amince da shi.

Da ta ke yanke hukuncin mai shari’a Maimuna Abubakar ta amince da wadanda suka shigar da karar sannan ta soke zaben fidda-gwani da aka gudanar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!