Labarai
Karkatar da kuɗaɗen haraji ya sanya jihar Kaduna ta yiwa Kano fintinkau – Usman Aliyu
Wani mai sharhi da kuma nazarin dokokin ƙasar nan ya bayyana cewa abinda ya jawo jihar Kaduna tafi jihar Kano tara kudin haraji shi ne ƙin bayyana kuɗin ga hukumomin da abin ya shafa.
Malam Usman Aliyu ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala shirin “Barka da Hantsi” na nan Freedom radiyo wanda yayi duba akan yadda jihar nan za ta gyara harajinta.
Malam Usman Aliyu ya ce “abin mamaki ne a ce jihar Kano tayi baya a bangaren tara kuɗaɗen harajin ta, wanda hakan na nuni da cewa dukkan kuɗaɗen da take samu suna zuwa inda bai kamata ba”.
Ya ƙara da cewa idan akai duba da irin harajin da jihar ke tarawa a ɓangaren kasuwanni da masana’antu ba za a taɓa haɗata da jihar Kaduna ba a ɓangaren haraji.
Malam Usman Aliyu ya kuma ce “da ana saka kuɗaɗen a cikin asusun gwamnati kamar yadda sauran jihohin ke yi da jihar Kano ita ce kan gaba wajan samar da kuɗin ta”.
Ya Ƙara da cewa kamata yayi gwmanatin tarraya ta ci gaba da karba harajin VAT ba wai a barshi a hannu gwmanatin jihohi ba duba da yadda a ke canja alakarsu.
wannan ya biyo yadda majalisar dokokin jihar Kano ta aike da sammaci ga shugaban hukumar tattara haraji sakamakon wani rahoto da wata kungiya ta fitar da cewa jihar kaduna tafi jihar Kano samun ƙudaden shiga.
You must be logged in to post a comment Login