Labarai
Karon Farko Yar Najeriya Ta Zama Gwarzuwar Shekara A Jami’ar Cyprus
Wata daliba ‘yar Najeriya, Mai Suna Ummukulsum Ibrahim Adamu, ta zama babbar daliba ta 3 a gaba dayan cikin daliban tsangayar tattalin arziki da kimiyyar gudanarwa da ke jami’ar Gabas ta Tsakiya, Arewacin kasar Cyprus.
Tsangayar Ilimin Tattalin Arziki da Kimiyyar Gudanarwar ta ƙunshi tsangayoyi, 9 inda Jami’ar ta yaye ɗalibai sama da 900 a bana.
Ummukulsum Ibrahim Adamu ‘yar asalin jihar Jigawa ta samu lambar yabo da maki 4.00. daga maki 4.00 da ake bukata a 2023-2024.
Hakan na cikin wasu hotuna na Ummukulsum Ibrahim Adamu tare da iyayenta, yayin bikin karramawar.
Matashiyar mai shekaru 20 da ta kammala karatun digiri, ta samu kyaututtuka daga jami’ar sakamakon kwazon data nuna.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan shi ne karo na farko da ɗan Najeriya ya samu irin wannan lambar yabo daga jami’ar.
You must be logged in to post a comment Login