Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu-yanzu: Ganduje ya bada umarnin rufe makarantun Kano

Published

on

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin rufe makarantun jihar bakiɗaya.

Kwamishinan ilimi na jihar Sanusi Sa’idu Ƙiru ne ya sanar da hakan ga Freedom Radio.

Ƙiru ya yi kira ga iyayen yaran da ke makarantun kwana kan su gaggauta dawo da ƴaƴansu gida.

Sai dai kwamishinan bai bayyana dalilin rufe makarantun ba.

Amma wata majiya ta shaida wa Freedom Radio cewa an rufe makarantun ne saboda dalilan tsaro.

Hakan na zuwa ne kwanaki huɗu bayan da ƴan bindiga suka sace ɗaliban makarantar sakandire a Katsina.

Tuni dai jihar Zamfara ta rufe wasu makarantu a jihar, yayin da jihohin Kaduna da Jigawa suka rufe makarantu saboda sake ɓarkewar annobar Corona.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!