Labarai
KAROTA ta kama babbar mota makare da giya
Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta ce ta chafke wata mota makare da giya da darajar kudinta ya zarta miliyan 15.
Jami’an hukumar ta KAROTA ne dai suka bi motar da ke makare da katan din giya sama da dari uku, a kan titin Zaria da misalin karfe 3 na rana bayan da driben motar ya isa yankin Unguwar Sabon gari.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in yada labarai na hukumar ta Karota Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa, inda ta ce ko da jami’an na KAROTA suka lura direban motar hiya ya dauko ne kuma suka nemi dauki jami’an ‘yan sanda , wanda da tainakon su ne kuma suka cimma nasarar kame motar.
Direbobi sun maka KAROTA da ‘Yan sanda a gaban kotu
KAROTA ta baiwa jami’in ta kyautar kudi mai tsoka
KAROTA tayi wawan kamu a kasuwar Singa
Sai dai ya ce ko da Direban motar da sauran mutanen ciki suka lura jami’an ‘yan sanda da na KAROTA na bin su ne kuma suka tsere tare da barin motar a nan.
Sanarwar ta kuma kara da cewa duk jami’in Karotar da ya tallafawa jami’an tsaro wajen chafke mutanen da ke shigowa jihar Kano da muggan kwayoyi da kuma giya yana da kyauta mai tsoka.
You must be logged in to post a comment Login