Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

KAROTA ta baiwa jami’in ta kyautar kudi mai tsoka

Published

on

Hukumar KAROTA ta jihar Kano ta baiwa wani ma’aikacin ta dake kula da shukokin hukumar kyautar naira dubu dari sakamakon kokarinsa wajen kula dasu.

Jami’in hukumar mai suna Ahmad Aminu da aka fi sani da suna Kurungu ya bayyana jin dadinsa  a ya yin zantawarsa da wakilin Radio Freedom Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa yau a hukumar.

Ahmad Aminu ya kuma kara da cewa ya shafe sama da shekaru shida yana aikin kula da shuke-shuke a hukumar ta KAROTA wanda hakan yasa shugaban hukumar ya bashi wannan kyautar kudi masu yawa.

Ahmad Aminu yace bayan ya karbi kyautar kudin daga shugaban hukumar KAROTA Baffa Babba Danagundi, shima ya dauki naira dubu talatin ya baiwa abokinsa da suke aikin tare ya kuma sake rarrabawa sauran abokan aikinsa na gidan wasu daga cikin kudin domin su sanya masa albarka.

Ahmad Aminu ya kuma sha alwashin cigaba da hidimtawa hukumar dukkannin shuke-shuke na KAROTA, kasancewar dama an dauke shine domin yai musu hidima.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!