Labarai
KAROTA ta karyata jita-jitar hana kasuwancin a bakin kasuwar Abubakar rimi
Hukumar Kula da Zirga zirgarni Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta karyata jita-jitar da wasu jama’a ke yadawa na Hukumar ta hana hada-hadar kasuwanci a kasuwar Rimi
Hakan na kunshe ne ta cikin sanarwar da Mai magna da yawun hukumar Nabulisi Abubukar Kofar Na’isa ya turawa Freedom Radio.
Sanarwar ta Kuma ce, “KAROTA bata hana kowa ya yi kasuwancinsa ba, amma dole ne kowa ya bi tsarin doka da oda”.
“Ya kuma zama wajibi ta karyata jita-jitar da ake yi na hana kasuwancin a kasuwar ta Rimi bayan da jita-jitar hana kasuwancin ta karade kafafen sada zumunta”.
Wace tace “kowa ya ci gaba da gudanar da kasuwancinsa amma ya zama wajibi a daina kasa kaya a kan titi saboda gujewa afkur hadura da cunkoson a kan wannan hanya”.
KAROTA ta kuma mika godiya bisa da hadin kan da Shugabancin kasuwar ke bayarwa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Rahoton: Abubakar Tujjani Rabi’u
You must be logged in to post a comment Login