Labaran Kano
KAROTA ta musanta jita-jitar sace kudin hukumar
Hukumar kula da zirga zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta musanta zargin cewa ‘yan Yahoo wato masu kutse’ sun sace kudin hukumar da ta tara, hasalima hukumar ta KAROTA ta mika sunayen wadanda take zargi da yada jita-jitar ga hukumomin tsaro domin fadada bincike.
Shugaban Hukumar KAROTA Baffa Babba Danagundi ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake kaddamar da fara saka Na’urar Tracker da kuma bada shaida wato ID Card a baburan Adaidaita Sahu na jihar Kano.
Baffa Babba Danagundi ya kara da cewa yayi mamaki kan yadda yaji ana yada jita-jitar cewa wai ‘yan Yahoo Yahoo sun kwashe kudaden hukumar wanda yace labarin bashida tushe bare makama.
Shugaban Hukumar KAROTA ta Kano Baffa Babba Danagundi ya nanata cewar abun kunya ne ma ace an sace kudin hukumar ta Karota domin a hannun banki kudaden suke ba’a wajen KAROTA ba, don haka ko da ma hakan ta faru banki ne ke da asara biyan kudaden bawai Hukumar KAROTA ta.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito Baffa Babba Danagundi na cewa hukumar KAROTA bazata zuba ido ana yada jita jitar karya ba, ga hukumar domin zasu cigaba da daukar mataki akan duk masu yada labaran karya akan hukumar.