Labaran Kano
KAROTA tayi wawan kamu a kasuwar Singa
Hukumar kula da zirga zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta kama gubatacciyar Fulawa sama da Tirela uku a kasuwar Singa da ake sayarwa mutane a nan Kano.
Shugaban Hukumar Karota na jihar Kano Baffa Babba Danagundi ne ya bayyana hakan a yau lokacin da yake zantawa da manema labarai da yammacin yau Laraba.
Baffa Babba Danagundi ya kara da cewa KAROTA ba zata lamunci cigaba da cutar da mutanan Kano ta hanyar sayar musu da kaya marasa kyau da kuma kwayoyi wanda za su iya cutar da lafiyar mutane.
Shugaban hukumar Baffa Babba yace kafin wawan kamun sun sami bayanan sirri kan cewa a na sayar da gurbatacciyar fulawar ne a kasuwar ta Singa wanda yasa suka nemi izinin Kotu kuma ta basu dama domin kwashe su.
Baffa Babba Danagundi ya kuma yi kira ga al’umma dasu rika kai rahotan duk irin wadannan gurare domin daukar mataki akan su.
Ana zargin KAROTA da haddasa hatsari a titin Zariya
Da sahalewar ‘yan kasuwar waya ta farm Center- KAROTA
Hukumar Hisbah ta Kano ta cimma yarjejeniyar aiki da KAROTA
Yana mai cewa abun takaicin shi ne yadda suke zargin wani babban dan kasuwa da hannu wanda ya gudu lokacin da suka kai samaman amma da zarar sun ganoshi za su fadi sunan sa.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito Baffa Babba Danagundi na cewa zasu baiwa duk wani mutum kyauta mai tsoka daya kawo rahotan guraren da ake sayar da kaya marasa kyau domin magance matsalar baki daya a fadin Jihar Kano.