Labarai
Karrama ni tamkar kalubale ne -Abdullateef Jos
Manajan labarai na nan tashar Freedom Radio Malam Abdullateef Abubakar Jos, ya bukaci ‘yan jarida da sauran al’umma da su kara zage dantse wajen gudanar da ayyukansu tsakani da Allah.
Malam Abdullateef Abubakar Jos, ya bayyana hakan ne jim kadan bayan da ya karbi shaidar karramawa da kungiyar masu bukata ta musamman ta ba shi.
Da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kyautar, ya bayyana cewa ya dauki kyautar a matsayin kalubalen da zai kara zaburar da shi wajen kara kaimi a gudanar da aikinsa.
Kungiyar dai ta raba kyaututtuka da lambar girmamawa ne yayin taron bikin ranar masu bukata ta musamman da ake gudanarwa a kowacce ranar 3 ga watan Disambar kowacce shekara.
A yayin taron dai kungiyar ta karrama mutane da dama da suka hadar da Hajiya Halima Shekarau da kwamishinan lafiya na jihar Kano da shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi na kasa kwamared Ibrahim Khalil da sauran mutane da dama.
Da yake jawabi yayin taron shugaban karamar hukumar Nassarawa kuma shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi na jihar Kano Lamin Sani Kawaji, wanda ya kasance mai masaukin baki a taron, ya bayyana cewa zai yi dukkan mai yiwuwa wajen bibiyar gwamnatin don ganin tana aiwatar da dokar masu bukata ta musamman da ta kafa tun a baya.
A nata jawabin, shugabar kungiyar masu bukata ta musamman shiyyar arewa maso yamma Bilkisu Ado Zango, ta ce akwai bukatar gwamnati ta samar musu da wasu mukamai a gwamnatance wanda hakan ne zai tabbatar musu da cewa gwamnatin tana tafiya da su.