Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

FMAN: Malaman gona su kara himma a kan noma – Sabo Nanono

Published

on

Ministan kula da harkokin noma, Muhammad Sabo Nanono ya bukaci malaman gona da su kara azma wajen koyar da manoma sabbin dabaru domin bunkasa harkokin noma a Najeriya.

Sabo Nanono ya bayyana haka ne yayin taron manoman alkama da kungiyar masu sarrafa fulawa ta kasa ta gudanar da taron bayar da sabbin nau’in irin alkama a ranar Litinin a karamar hukumar Danbatta a jihar Kano.

Ministan ya kuma ce, “Gwamnatin shugaba Buhari ta na ci gaba da bada hadin kai da goyon baya ga kungiyoyin manoma da dama domin Najeriya ta samu damar noma abincin da zata ciyar da kanta.”

A nasa jawabin shugaban kungiyar masu sarrafa fulawa ta kasa FMAN wanda ya samu wakilcin, Serah Hoba, ta ce manufar shirya taron shine taimakawa wajen bunkasa harkar noman alkama tare da bada gudunmowa ga manoma, domin su ma su shigo cikin harkar noman alkama domin ingantata alkama a kasar nan.

Ta ce, ”Kungiyar ta na da cibiyoyi a kananan hukumomin Danbatta da Garun Malam da Bunkure da Kura da kuma Ajingi, kungiyar za ta ci gaba da sayen alkamar daga hannun manoman idan sun kammala noman.”

Wani daga cikin manoman alkamar, Abdullahi Abubakar Danbatta ya yaba wa kungiyar bisa irin tallafin da suka samu na ingantaccen irin alkamar duba da yadda suka fuskanci kalubale a shekarun baya amma yanzu kungiyar ta kawo masu sauki.

Kungiyar ta kuma nemi hadin kai da goyon bayan gwamnati a kokarinta na kawo sauyi a harkar noman alkama ta hanyar bijiro da dabarun bada tallafi da basussoka da horo da kuma kyautar iri ga manoman don bunkasa ayyukan noman na su a wannan zamanin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!