Labarai
kasar Saudia ta baiwa yan arewa maso gabashin kasar nan tallafin kayayyakin jinkai
Kasar Saudi Arebiya ta baiwa kasar nan tallafin kayayyakin jin kai da kudin-su suka kai naira biliyan uku da miliyan dari shida domin rabawa ga mutanen da rikicin Boko-haram ya raba da gidajen su a yankin arewa maso gabashin kasar nan.
Ministan tsaron kasar nan Burgediya Janar Mansur Dan Ali mai ritaya ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke mara ba ga wakilan kasar Saudiya wadanda suka ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja.
Ya kuma shaidawa tawagar ta Saudiya cewa za a tabbatar da cewa kayayyakin sun isa ga wadanda aka turo domin su.
Ya kuma ce ci gaba da samun fituntunu daga nan zuwa can da kuma kwararowar ‘yan gudun hijira da abaya suka tsere zuwa makwabciyar kasar nan Kamaru na daga cikin manyan dalilan da suke kara ta’azzara matsalolin jin kai a yankin.
Cikin kayayyakin da kasar ta Saudiya ta ba da tallafinsu sun hada da: Abinci da kayayyakin kula da lafiya da kuma kayayyakin ilimi.
Cikin tawagar kasar Saudiya da suka ziyarci ministan sun hada da: Mataimakin daraktan hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar Nasir Bin Mutlak da Khalid Bin Abdurrahman Al Mani da kuma Muhammed Bin Addidah Al Namlah.