Labarai
Kasar Saudiyya da Najeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar aikin Hajjin bana

Shugaban hukumar alhazai ta Najeriya Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da mataimakin ministan Hajji na Saudiyya Abdulfatah Mashat ya wakilci Saudiyyar.
Gwamnatin Najeriya ta ƙulla yarjejeniyar gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 ne yayin wani biki a birnin Jeddah da ke kasar ta Saudiyyar.
Hukumar alhazan Najeriya Nahcon ta ce yarjejeniyar hujja ce cewa kasar ta shiga jerin ƙasashen da za su gudanar da aikin ibadar a bana.
Zuwa yanzu babu tabbas game da adadin maniyyatan da za su je Saudiyya a bana, musamman saboda sanarwar Nahcon ta watan Oktoba cewa hukumomin Saudiyya sun rage yawan kujerun Hajjin na Najeriya daga 95,000 zuwa 66,000.
Hukumar ta ce Saudiyya ta ɗauki matakin ne saboda Najeriya ba ta cike dukkan guraben da aka ware mata a bara, inda aka samu giɓin alhazai 35,872.
You must be logged in to post a comment Login