Labarai
Kasashen duniya na cigaba da sukar shirin kasar Isra’ila
Kasashen duniya na cigaba da Allah wadai da matakin kasar Isra’ila na kaddamar da shirin mamaye wani bangare da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan, yayinda suke cewa hakan bay a bisa tsarin doka yayinda ya sabawa manufar kasar.
A jiya Laraba ne Benjamin Netanyahu ya tsayar da matsayin ranar da Isra’ila za ta fara jaddada ikonta kan yankunan Yahudawa da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan.
Matakin na Isra’ila zai yi dai-dai da kudirin Shugaban Amurka Donald Trump na zaman wanzar da lafiya – matakin da zai kawo karshen tsawon shekarun da aka shafe ana rikici tsakanin Isra’ilawa da Falasdinawa da ya kaddamar a watan Janairu.
Ana yi wa yankunan kallon haramtattu karkashin dokokin kasa-da-kasa duk da cewa Isra’ila – da Amurka karkashin mulkin Trump – sun musanta hakan.
Mataimakin shugaban kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International a Gabas ta Tsakiya Saleh Hijazi ya ce: bisa tsarin dokar kasa da kasa cewa mamayar yanki ya haramta tare da cewa Isra’ila na kokarin yiwa dokokin kasa-da-kasa karan tsaye idan har ta dage a kan shirinta.
You must be logged in to post a comment Login