Manyan Labarai
Kashi 50 na cin zarafin dan Adam na faruwa ne a matakin Iyali
Hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa dake nan Kano tace yawancin rahotanni da suke samu na cin zarafin bil’ Adam ana faruwa ne a gidaje.
Shugaban hukumar kare hakkin dan Adam na Jahar Kano Shehu Abdullahi ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da filin Barka da Hantsi a cikin bikin ranar kare hakkin dan Adam ta Duniya da ake bikin a yau.
Tun a ranar 10 ga watan Disambar 1948 ne majalisar dinkin Duniya ta ware domin kare hakkin dan Adam.
A nasa bangaren shugaban gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan Adam ta Jahar Kano Kwamared Abdullahi Haruna Ayagi yace kokarin da kungiyar su take yi na kare hakkin dan Adam shi ne wayar da kan al’umma da kuma koyar da yara kanana matsalolin rayuwa.
Yace idan sun samu labarin cin zarafi suna hada kai da hukumar ‘’Yansanda da sauran jami’an tsaro domin magance matsalar.