Ƙetare
Kashim Shettima ya sake mika bukatar bai wa Najeriya kujera ta dindindin a MDD

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya sake mika bukatar a bai wa Najeriya kujera ta dindindin a gaban Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, a wani bangare na babban taron majalisar karo na 80 da ake gudanarwa a birnin New York na Amurka.
Shettima, ya ce, Najeriya na da cancanta saboda gudunmawar da ta dade tana bayarwa wajen samar da zaman lafiya a Afirka da duniya, in da ya buga misali da gudunmawar da kasar ta bayar a kasar Congo a shekarar 1960 da kuma kasashen Liberia da Saliyo da Sudan da kuma kawo ƙarshen wariyar launin fata a Afirka ta Kudu.
Lamarin da masana tsaro ke ganin matsalolin tsaro da cin hanci da halin tattalin arzikin Najeriya na iya zama ƙalubale wajen cimma wannan buri.
Duk da haka, Najeriya na ganin kujerar za ta ƙara tasirinta tare da kare muradun Afirka a harkokin duniya.
You must be logged in to post a comment Login