Labarai
Kaso 90 na motocin da ake shigo da su Najeriya ta barauniyar hanya ce –Hameedd Ali
Shugaban hukumar kwastan Col. Hameed Ali ya bayyana cewa kaso 90 cikin 100 na motocin da ake shigowa da su Najeriya ana shigo da su ne ta haramtacciyar hanya.
Hameed Ali a bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, ya kara da cewa da dama motocin da ake tallansu a fadin kasar nan ana shigo da su ne ta barauniyar hanya.
Haka kuma y ace a wani samame da suka kai wa dilolin motoci a yan kwanakin nan a sassan Najeriya, ya tabbatar musu da hakan cewar ana shigo da motocin ne ba bisa ka’iada ba.
Hameed Ali ya ce kasar nan na bukatar hanyoyin kudaden shiga, don haka yana da muhimmanci su tabbatar sun karbi kudaden haraji akan dukkanin wadanda suka shigo da mota ta barauniyar hanya.
Ya ce suna yukurin amfani da dama tare da tabbatar da cewar dukkanin motocin da aka shigo da su ta iyakar najeriya sun bi ka’idoji, wanda tilas zai basu damar biyan kudaden hanyar da ta dace.