Labarai
Kason Kano na rabon arzikin kasa na watan Maris ba zai biya albashi ba – Chidari
Shugaban majalisar dokokin jihar Kano Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya ce, halin matsin tattalin arziki da kasar nan dama duniya baki daya suka shiga, ya sanya gwamnatin Kano ba za ta iya aiwatar da wasu muhimman ayyukan raya kasa ba.
A cewar sa ko da kason da gwamnatin Kano ta karba na rabon arzikin kasa daga asusun tarayya a wannan wata na Maris ba zai ma iya biyan albashin ma’aikata ba, ballantana har a aiwatar da ayyukan raya kasa da su.
Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na nan tashar freedom radio wanda ya gudana a ranar laraba.
‘‘Idan son ran mu ne to duk ayyukan raya kasa a aiwatar da su amma kamar yadda kowa ya sani ne duniya baki daya ana fuskantar matsalar tattalin arziki sanadiyar bullar cutar covid-19, saboda haka gwamnati ba ta da isassun kudade da za ta iya aiwatar da ayyukan raya kasa’’
‘‘Misali ko da a wannan wata kudin da jihar Kano ta karba daga asusun tarayya ba zai kai a iya biyan albashin ma’aikata ba ma balle har ayi wasu ayyuka’’ a cewar shugabn majalisar dokokin jihar ta Kano.
You must be logged in to post a comment Login