Labarai
kasuwar hannun jari kasuwa ce da bata da tabbas a bangaren farashi
Kotun shari’ar masu zuba hannun jari shiyyar jihar kano ta ce daga shekarar 2003 zuwa yau ta karbi korafe-korafe daga wurin jama’a masu kara kan hannun jarin da suka zuba a kamfanoni daban-daban da ya kai kimanin naira biliyan dari uku da casa’in.
Magatakardar kotun na kasa Barrister Habu Yarima Saleh ne ya bayyana hakan a cikin shirin Duniyarmu A Yau na nan tashar Freedom Radiyo da ya mayar da hankali kan yadda ya kamata a gudanar da kasuwancin hannun jari kan tsarin doka.
Barrister Habu Yarima ya ce kasuwar hannun jari kasuwa ce da bata da tabbas a bangaren farashi, ta yadda ake iya samun hawa da sauka a kowane lokaci, wanda hakan shi ke kawo yawaitar matsaloli daga bangaren masu zuba hannayen jari.
A nasa bangaren Babban Sakataren kotun shari’ar hada-hadar hannun jari dake nan kano Barrister Kabiru Kiru da ya kasance a cikin shirin ya bayyana cewa sakacin mutane na rashin fadada bincike na taka rawa wajen fadawar su hannun yan damfara da sunan zuba hannun jari.
Ya ce ya kamata mutane su san cewa babu wani kasuwanci da yake kawo irin ribar da za ta ninkawa mutum kudinsa cikin dan kankanin lokaci kamar yadda wasu bara gurbin kamfanonin hannun jarin ke alkawartawa mutane.
Wakilinmu Mu’azu Tasi’u Abdurrahman ya rawaito cewa baki dayan bakin sun yi kira ga al’umma da suke da niyyar zuba hannun jari a wani kamfani da su rika neman shawarar hukumar kula da zuba hannayan jari ta kasa wato SEC don tabbatar da ingancin kamfanonin kafin zuba kudinsu don gudun fadawarsu hannun bata gari.
You must be logged in to post a comment Login