An Tashi Lafiya
Katse layukan sadarwa a Zamfara ya fara sa al’ummar Jihar cikin halin ƙaƙa na kayi
Yayin da jami’an tsaron Jihar Zamfara ke ci gaba da ragargaza ƴan bindiga a Jihar, tun bayan katse layukan waya a Jihar, al’ummar garin na cigaba da kokawa kan matsatsin da suka shiga musamman a bankuna.
Daman dai an ɗauki wannan mataki ne da zummar daƙile illar masu bada bayanai ga ƴan ta’adda.
Wasu daga cikin mazauna garin sun bayyawa Freedom cewa suna kira ga hukumomi da su samar musu da hanyoyin samun kuɗaɗen su ta hanya mafi sauƙi a bankuna.
Gwamnan Jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle yace ya tsawatar wa bankunan domin su samawa al’umma mafita, ya kuma ƙara da cewa “na ji koken mutane cewa babu natwak, babu kuma kuɗi acikin Jihar, ni da kaina naje bankunan nace dole suyi tanadi na daban, yadda al’umma za su samu sauƙi”.
A dai ranar 3 ga watan Satumba ne hukumar sadarwa ta katse layukan waya a Jihar, zuwa tsawon makonni biyu, wanda zai ƙare a ranar jumu’a mai zuwa 17 ga watan Satumba.
You must be logged in to post a comment Login