Labarai
Katsina: Mutane 2 sun rasu sakamakon zanga-zangar da matasa suka gudanar

Aƙalla mutane biyu ne suka mutu bayan wata zanga-zanga da matasa suka gudanar a ƙauyukan Danjanku, Dantashi da Dayi na ƙaramar hukumar Malumfashi, Jihar Katsina.
Zanga-zangar ya biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kai a ranar Litinin, inda suka kashe mutum ɗaya suka kuma tafi da wasu 17 duk da yarjejeniyar zaman lafiya da ke tsakanin gwamnati da yan fashin dajin.
Rahotanni sun nuna cewa matasan yankin sun fito zanga-zangar ne da safe inda suka toshe hanyar Funtua–Katsina domin nuna bacin ran su kan tsananin hare-hare da kuma gazawar gwamnati wajen kare su.
Sai dai lamarin ya rikide ya zama tashin hankali bayan isowar jami’an tsaro, inda suka bude wuta suka kashe mutane biyu tare da jikkata wasu biyu.
Mai unguwar Danjanku, Alhaji Tanimu Almakiyayi, ya tabbatar da faruwar harin inda yace suna rayuwa cikin fargaba, yayin da wasu mazauna suka zargi dakarun tsaro da kashe masu zanga-zangar.
A wani hari daban a Bakori, an kashe ɗan sanda ɗaya, aka jikkata wasu biyu, yayin da jami’an tsaro suka ce sun hallaka wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne su tara.
You must be logged in to post a comment Login