Labarai
Katsina: Sojoji sun ceto mutane 76 daga hannun yan Bindiga

Hukumomi a jihar Katsina sun ce sojoji sun yi nasarar ceto mutane 76 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su yawancin su kananan yara a wani farmaki da suka kai kan ‘yan ta’addan.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Katsina Nasiru Mua’azu ya ce farmakin ta sama a yanzu wata sabuwar dabara ce ta wargaza maboyar ‘yan bindigar da kuma kawo karshen kashe kashe da garkuwa da mutane don karbar kudun fansa da suka addabi mutanen da basu ji ba basu gani ba.
Ana kyauta zaton mutanen da aka ceto suna daga cikin wadanda ‘yan bindigar suka yi awon gaba da su bayan wani hari da suka kai kan wani masallaci a unguwar Mantau a makon da ya gabata inda suka hallaka mutane 50.
Ta’asar ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram tsawon shekaru ya addabi yankunan arewacin Najeriya duk da kokarin da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu da kuma wanda ya gabace shi suka yi na shawo kan hare haren.
You must be logged in to post a comment Login