Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kawu Sumaila ya gabatar da kudirin neman soke jinginar filin jirgin Kano

Published

on

Tun bayan da Sanatan Kano ta Kudu Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila ya gabatar da ƙudirin soke batun jinginar da filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu dake nan Kano, al’umma ke cigaba da bayyana ra’ayoyinsu.

A zaman majalisar na jiya Alhamis ne sanata Kawu Sumaila ya gabatar da ƙudirin a zauren majalisar dattawa, yana mai cewa an tafka kura-kurai wajen shirya bada jinginar filin jirgin.

Tun a ranar 17 ga watan Mayun daya gabata ne dai majalisar zartarwa ta amince da baiwa wani kamfanin Amurka jinginar filayen jiragen saman.

Sanata Kawu ya ce alhakin lura da harkokin filayen jiragen saman kasar nan ya ta’allaƙa ne kan hukumar lura da tasoshin jiragen kasa wato FAAN kamar yadda dokar da ta kafasu ta yi tanadi, don haka ba sa ƙarƙashin ma’aikatar sufurin jiragen sama.

rahoton: Asma’u Muhammad Sani

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!