Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta hana kama Ganduje kan Bidiyon Dala

Published

on

Wata kotun tarayya ta hana kamawa tare da bincike ko kuma gayyatar tsohon gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje dangane da zargin da ake masa kan wani faifan bidiyon zarginsa da karbar cin hancin Dalolin Amurka.

Yayin zaman kotun a Juma’ar makon nan, ta hana dukkanin jami’an tsaro da suka hadar da DSS, Yan sanda rundunar tsaro ta Civil Defence, da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano daga gayyata ko Kuma kama tsohon Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ko iyalan sa ko Kuma Wani da aka gudanar da gwamnatin baya dashi, har sai zuwa ranar 14 ga wannan wata da kotun za ta saurari korafin da aka shigar gaban ta.

A baya-bayan nan ne hukumar karbar korafi da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano PCACC, ta gayyaci tsohon gwamnan domin amsa wasu tambayoyi kan zargin karbar rashawa da aka hasko shi a wani faifan bidiyo.

Sai dai tun a wancan lokaci gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya musanta batun, inda yanzu kuma bayan gayyatarsa da hukumar ta yi sai ya garzaya kotu domin kalubalantar gayyatar tasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!