Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kazafin maita ya kawo cikas ga soyayyar wasu masoya a Kano

Published

on

Soyayyar wasu matasa biyu Aliyu Tukur da Maryam Muhammad ta shiga cikin tasku bayan da dan uwan Maryam din ya yi kazafin Maita ga saurayin nata.
Wannan al’amari ya faru ne a karamar hukumar Bebeji dake nan Kano, inda Ukasha Muhammad ya rika yadawa a garin cewa saurayin kanwarsa Aliyu maye ne.
Wannan kazafi ya janyo mutanen na kyamatar Aliyu da danginsa kamar yadda ya shaidawa Freedom Radio, wanda hakan ta sanya yayi korafi ga kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Right dake nan Kano.
Yayi wani zaman sulhu da aka gudanar jiya Laraba, Ukasha Muhammad ya nemi afuwar Aliyun a gaban mai unguwa da kuma wakilan kungiyar kare hakkin da adam.

Karin labarai:

Hukumomi sun rufe asibitin Maita a Kano

Kotu ta fara sauraron shari’ar maita a Kaduna
Shugaban kungiyar kare hakkin da adam din Karibu Yahya Lawal Kabara ya shaidawa Freedom Radio cewa, za su je can garin sannan a tara jama’a Ukashan ya zo ya kara warware maganar a gaban su.
Ita ma a nata bangaren Maryam Muhammad ta shaidawa Freedom Radio cewa, furucin dan uwanta yaso ya kawo cikas ga soyayyar su, amma a yanzu ta fahimci komai tana kuma rokon masoyin nata Aliyu da ya yafe masa, sannan soyayyar su tana nan daram za a cigaba da tsinkar fure.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!