Ƙetare
Kazamin fada ya barke tsakanin sojin Sudan da mayakan RSF

Rahotanni sun bayyana cewar an gwabza ƙazamin fada a yankin kudancin tsakiyar Sudan tsakanin rundunar sojin kasar da kuma kungiyar RSF.
Sojojin sun ce sun ƙwace garin Mabsouta da ke kudancin Kordofan, amma kuma dakarun rundunar da ke Arewacin Kordofan din na fama da harin jiragen sama marassa matuka.
Mazauna babban birnin – El-Obeid, sun ce sun ga hayaki na tashi daga wani sansanin soji da ke birnin.
Duk wani yunƙuri na dakatar da bude wuta ya ci tura inda bangarorin biyu ke kafewa kan wasu sharudda da ba za su yiwu ba.
Jihohin Kordofan din uku sun kasance fagen-daga a yakin basasar Sudan din na wata talatin , inda yanzu kungiyar ta RSF ta kame Darfur.
You must be logged in to post a comment Login