Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Ƙetare

Za a bukaci fiye da Dala biliyan 3 don samar da agajin gaggawa a Sudan- MDD

Published

on

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, za a bukaci  sama da Dala biliyan 3, domin samar da agajin gaggawa a Sudan mai fama da rikici yayin da ake fargabar sama da mutane miliyan daya za su tsere zuwa kasashen da ke makwabta da kasar a bana.

Haka kuma ta ce, a yanzu ana sa ran za a bukaci fiye da Dala biliyan 2,  don samar da taimako ga Sudan din daga Dala biliyan 1 da aka kiyasta a karshen shekarar da ta gabata.

Yanzu haka dai an ci gaba da gwabza fada ne a kasar tun bayan  ranar 15 ga Afrilu tsakanin babban hafsan sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar rundunar kai daukin gaggawa ta RSF.

Kimanin mutane 1,000 aka kashe, a ciki da wajen Khartoum babban birnin kasar da kuma yankin yammacin Darfur da ya samu hargitsewa a cewar likitoci.

Fiye da mutane 5,000 kuma sun jikkata, yayin da wasu miliyoyi ke ci gaba da zama a killace cikin gidajensu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!