Labarai
Kebbi: Rundunar yan sanda ta tura jami’ai na musamman don aikin nemo daliban GCSS Maga

Rundunar yan sandan kasar nan ta tura jami’ai na musamman don haɗa kai da sojoji da ‘yan sa-kai wajen nemo ɗaliban da aka sace a makarantar sakandiren ‘yan mata ta Government Girls Comprehensive Secondary School, Maga da ke ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Nafiu Abubakar Kotarkwashi, ya ce tawagar na bincike a hanyoyin da ’yan bindiga suka bi da dazuzzuka domin ceto ɗaliban tare da kama waɗanda suka kai harin.
A cewar runduna ’yan sandan, a ranar 17 ga watan Nuwamba, 2025, da misalin ƙarfe 4 na asuba, wasu ’yan bindiga ɗauke da makamai suka kutsa makarantar, suna harbe-harbe.
Rundunar ta ce jami’an ta da ke wajen sun yi artabu da su, amma ’yan bindigar sun tsallaka katangar makarantar tare da sace ɗalibai 25, baya ga kashe wani mutum mai suna Hassan Makuku, tare da jikkata wani Ali Shehu.
You must be logged in to post a comment Login