Labarai
Kebbi: Yan Bindiga sun kashe mataimakin shugaban makaranta a harin da suka kai

Yan bindiga sun kai hari a makarantar sakandaren ‘yan mata ta gwamnati GGCSS, Maga, a yankin Danko Wasagu na Jihar Kebbi, inda suka kashe mataimakin shugaban makarantar, Hassan Yakubu Makuku, tare da sace ɗalibai dahar zuwa yanzu ba a tantance adadinsu ba.
Wani mazaunin Maga, Aliyu Yakubu, ya ce ‘yan bindigar sun dirar wa makarantar ne da misalin ƙarfe 5 na safiyar Litinin inda Harin ya jefa mazauna yankin a cikin firgici
A cewar majiyar shugaban makarantar, Makuku, an harbe shi ne yayin da yake ƙoƙarin hana yan bindigar yin awon gaba da dalibansa .
A lokacin da ake tattara wannan rahoto, rundunar ‘yan sanda ba ta ce komai ba game da lamarin, domin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Nafiu Abubakar, bai amsa kiran da wakilin Jaridar Daily Trust yayi masa ba
You must be logged in to post a comment Login