Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kisan Ƴar Aiki: Bayan kiraye-kiraye ƴan sanda sun saki hoton wadda ake zargi

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta saki hoton matar da ake zargi da yin ajalin ƴar aikinta.

Mai magana da yawun ƴan sandan Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya fitar da hoton ta shafinsa na Facebook da misalin ƙarfe 1:50 na ranar Lahadi.

Ku kalli hoton a ƙasa.

ZARGIN KISAN ‘YAR AIKI

MUN GURFANAR DA FATIMA HAMZA ME SHEKARU TALATIN A GABAN CHIEF MAGISTRATE COURT MAI LAMBA 8 DAKE GYADI GYADI KANO, AKAN ZARGIN KISAN KAI.

Posted by Abdullahi Haruna Kiyawa on Sunday, February 7, 2021

 

Wannan dai ya biyo bayan kiraye-kirayen da al’umma suka riƙa yi a kafafen sada zumunta kan ‘yan sanda su fitar da hotonta kamar yadda suke fitar da na waɗanda ake zargi da aikata laifuka.

Kiyawa ya ce, sun gurfanar da Fatima Hamza mai shekaru 30 a gaban kotu majistiri mai lamba da ke Gyaɗi-gyaɗi a Kano bisa zargin kisan kai.

Labarai masu alaka:

Kisan Ƴar Aiki: An nemi ƴan sanda su saki hoto da bidiyon wadda ake zargi

Kisan Ƴar Aiki: An gurfanar da wadda ake zargi a gaban kotu

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!