Labarai
Kisan Ƴar Aiki: An nemi ƴan sanda su saki hoto da bidiyon wadda ake zargi
Jama’a a kafafen sada zumunta na neman rundunar ƴan sandan Kano da ta bayyana hoto da bidiyon wadda ake zargi da kisan ƴar aiki.
Bisa al’ada dai rundunar ƴan sandan Kano ta kan yi holen mutanen da ta kama da zargin aikata laifuka cikin bidiyo kafin gurfanar da su a gaban kotu.
Shafin mai magana da yawun ƴan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa na Facebook cike ya ke da irin waɗannan faya-fayan bidiyo.
Na baya-bayan nan dai shi ne a ranar Jumu’a, inda ya wallafa wasu da ake zargi da laidi ciki har da mace, har ma yake cewa, ta cire takunkumin fuskarta, kamar yadda kuke gani a ƙasa.
Baya ga wannan a kwanakin baya, ya wallafa wasu da ake zargi da satar mutane waɗanda aka kama a unguwar Jaba da ke nan Kano, suma ciki har da mace kamar yadda kuke gani a wannan bidiyon da ke ƙasa.
Ba wai ga iya maza da mata kaɗai ne ƴan sanda ke sanya bidiyon su ba, a’a har da ƙananan yara, domin a wannan bidiyon da ke ƙasa ƙananan yara ne har da mai shekaru goma sha uku a duniya da ƴan sandan ke zargi da fashi a unguwar Ɗandago da ke Kanon.
Da alama wannan ya sanya jama’a ke jefa alamar tambaya kan yadda ƴan sanda suka ce sun samu hujjoji har sun gurfanar da wadda ake zargi da hallaka ƴar aikin a gaban kotu.
Sai dai kuma har kawo lokacin da muke haɗa wannan rahoto ba a ga sun fitar da bidiyonta ba kamar yadda suka saba, waje guda kuma sun fitar da bidiyon waɗanda ake zargi da satar keken ɗinki.
Wani abin mamaki ma shi ne yadda ƴan sandan suka yi bidiyo ga abokiyar aikin marigayiyar wadda ita ma yarinya ce ƙarama.
Sannan suka yiwa waɗanda suka taimaka wajen fitar da labarin bidiyo, amma har yanzu na wadda ake zargi bai fito ba.
Wani mai amfani da dandalin sada zumunta na Facebook mai suna Muhammad Inuwa Muhammad ya wallafa a shafinsa cewa.
“Ƴan sanda a jihar Kano in sun kama ɓarayin waya suna jere su, suyi musu bidiyo su yaɗa, amma sun kama wadda ake zargi da kashe ƴar aikinta sun ƙi su yi mata bidiyo”.
Ƴan sanda a jihar Kano in sun kama ɓarayin waya suna jere su suyi musu bidiyo su yaɗa, amma sun kama wadda ake zargi da kashe ƴar aikinta sun ƙi su yi mata bidiyo.
Posted by Muhammad Inuwa Muhammad on Friday, February 5, 2021
A nan kuma mai magana da yawun ƴan sandan Kano ne ya wallafa bayanin sakamakon bincikensu kan batun kisan ƴar aikin, da kuma batun cewa sun gurfanar da wadda ake zargi a gaban kotu.
Daga cikin masu tsokaci a kai, Adamu Ado Muhammad ya ce, “A zahirin gaskiya kamar yadda ake yaɗa sauran hotunan waɗanda ake zargi da laifi, ita ma ya kamata a saki hotonta duk duniya ta gani, wannan shi ne adalci”.
“Bana tsammanin adalci a saki hoton ɓarawon waya duniya ta gani, kuma a kasa sakin hoton wadda ake zargi da kisan kai”.
“Allah ya taimake ku, ya kare ku”.
Har zuwa lokacin da muke ci gaba da tattara wannan rahoto jama’a na ta yin tsokaci a kai, mu kuma muna ci gaba da bibiyar lamarin.
Mun tuntuɓi mai magana da yawun ƴan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa kan wannan batu, sai dai bamu samu ji daga gareshi ba.
Labarai masu alaka:
You must be logged in to post a comment Login