An Tashi Lafiya
Ko me Aisha Buhari take nufi da “A cire tsoro, a yi abin da ya dace”?
Uwargidan shugaban ƙasa Aisha Muhammadu Buhari, ta yi fashin baki kan wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram wanda ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta.
A ranar Lahadi ne uwargidan shugaban kasar ta wallafa bidiyon Ministan sadarwa da kula da tattalin arzikin fasahar zamani Isa Ali Pantami, inda ta sanya fefan bidiyon da aka nuna shi yana kuka tare da mai ja masa baki a wani wa’azi da ya yi a baya, kan wata aya mai da ke jan hankali kan abin da ya shafi tsoron Allah.
A karkashin bidiyo da ta wallafa na ranar Lahadin, Aisha Buhari ta rubuta cewa: “Tunatarwa ce, a cire tsoro a yi abin da ya dace.”
Sai dai wayewar garin ranar Litinin, uwargida Aisha ta yi karin harske kan abin da take nufi da wannan sakon. Inda ta ce “Tafsir na Malam kan tsoron Allah ne ba tsoron mutum ba! Da aka cire tsoro da son kai aka shiga jihar Zamfara, abubuwa sun fara kyau. Sai a dage a shigo sauran wurare da ke bukatan hakan.
You must be logged in to post a comment Login