Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Kun san abinda ya biyo bayan komawar Aisha Buhari Villa?

Published

on

A dai kwanakin baya ne fadar shugaban kasa ta maida martanai kan jita-jitar da ake yadawa kan Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi Yaji, sai gashi kwatsaham jiya daddare ta Iso kasar nan.

Bayan ta sauka a filin jirgin saman Nnamadi Azikiwe, Hajiya Aisha Buhari ta samu tarba daga Uwargidan gwamnan jihar Kogi Rashida Bello da mai baiwa shugaban kasa shawara kan sha’anin mulki ta mussaman Hajjo Sani da Uwargidan tsohon gwamnan jihar Nasarawa Mairo Al-Makura da dai sauran su.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewar da Isowar ta ta, da manema labarai suka tambaye ta menene dalilin da ya sanya ta bar kasar nan har na tsawon watanni 3, nan take ta kada baki tana cewa daman ta saba yin irin wannan hutun a duk shekara musamman ma a watan Yuni zuwa Yuli yayin da take zuwa take zama da ‘ya’yan ta.

Amma kuma a wannan lokacin Aisha Buhari ta jefi tsuntsu biyu da dutse daya, bayan samun damar zama da ‘ya’yan ta, ta kuma ga likita  a can Burtaniya, da ga nan kuma taje kasa mai tsarki don yin aikin Hajjin bana a cewar Aisha Buhari’’

A yayin jawabin da ta yi wa manema labarai jim kadan bayan da ta sauka, tayi gugar zana ga wacce ake zargin cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari zai Aura a ranar Juma’ar da ta gabata bayan da aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta.

Rahotannin sun bayyana cewar tun bayan kammala aikin Hajjin Bana ba’a sake ganin fuskar Uwar gidan shugaban kasa ba Hajiya Aisha Buhari ba.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa tun bayan kammala aikin Hajji Uwar gidan shugaban kasar ta ziyarci birnin Landan ana hasashen cewa kamar ta yi yaji ne, kasancewar ta jima tana sukan irin salon mulkin shugaba Buhari.

Na baya-bayan nan dai shine furucin da tayi a lokacin da ta ziyarci jihar shugaban kasar wato jihar Katsina, inda ta bayyana takaicinta kan yadda tace ‘yan arewa na baiwa gwamnatin kuri’a amma wasu al’umma daban ne ke cin gajiyar gwamnatin.

Rubutu masu alaka:

Shin Aisha Buhari tayi yaji?

Ina Aisha Buhari take?, fadar shugaban kasa ta yi martani

Aisha Bahari ta soki shirrin Gwamnatin tarayya na rage fatara

Har ila yau wasu na ganin cewar ba’a ganin fuskar ta a muhimman wurare tare da shugaban kasar ba, kamar taron majalisar dinkin duniya da aka kammala kwanannan da dai sauran su.

Sai dai wasu na zargin cewar uwar gidan shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari bata jituwa da wasu daga cikin manyan kusoshin gwamantin, wanda hakan ya sanya dagantaka tayi tsami a tsakanin su har ta kai ga tayi yaji.

Amma kuma Fadar shugaban kasa ta maida martani kan zargin da wasu ke yi cewa Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi yaji.

A cewar fadar shugaban kasar Aisha Buhari na da ‘yancin tafiya duk in da take son zuwa, kuma bata yi rikici da kowa ba a fadar shugaban kasar dake Abuja.

Bayanin haka ya fito ne ta bakin mai Magana da yawun ta Suleman Haruna ‘’cewa watannin 2 da ba’a ganin fuskar uwargidan shugaban kasar, ba yana nufin cewar babu fahimtar juna a tsakanin ta da maigidan ta ba ko kuma wasu jiga-jigan gwamnati mai ci’’, a’a illa kawai wasu ne ke kitsa labarun karya don tada fitina’’

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!