Connect with us

Labarai

Aisha Buhari ta nemi gafarar ‘yan Najeriya

Published

on

Mai dakin shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari ta nemi afuwan ‘ya’yanta da iyalanta da kuma ‘yan uwa da abokan arziki dama al’ummar kasar nan baki daya game da bullar wani faifan bidiyo a baya-bayan nan wanda ya nunata tana bayani kan matsalarsu ta cikin gida a fadar shugaban kasa.

A daya daga cikin faifan bidiyon an gano maid akin shugaban kasar tana jawabi da kakkausar lafazi kan iyalan gidan Mamman Daura, wanda ta ke bukatar cewa sai su kwashe ya nasu ya nasu su bar fadar shugaban kasa.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai Magana da yawunta, Suleiman Haruna.

Haka zalika Sanarwar ta ce shugaba Buhari ya kuma amince da nadin wasu masu taimakawa mai dakinsa Hajiya Aisha Buhari.

Kun san abinda ya biyo bayan komawar Aisha Buhari Villa?

Ina Aisha Buhari take?, fadar shugaban kasa ta yi martani

Shin Aisha Buhari tayi yaji?

Aisha Bahari ta soki shirrin Gwamnatin tarayya na rage fatara

Wadanda aka nadan sun hada da: Dr Mairo Almakura a matsayin mataimakiya ta musamman ga maid akin shugaban kasa kan harkokin shirin samar da zaman lafiya na kungiyar matan shugabannin nahiyar afurka da Muhammed Albishir mai taimaka mata kan harkokin kungiyar matan shugabanin na Afurka.

Sauran sune: Wole Aboderin mai taimakawa uwargidan shugaban kasa kan kungiyoyi masu zaman kansu da Aliyu Abdullahi mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da Zainab Kazeem mataimakiya kan ayyuka na musamman da kuma Funke Adesiyan mataimakiya na musamman kan harkokin wasu muhimman ayyuka.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!