Labarai
Ko mene ne makomar ‘yan marin da ake sakowa?
A ‘yan kwanakin nan ne, mahukunta ke ta sako matasan da ke daure cikin mari a gidajen gyaran tarbiyya da ke sassan jihohin Najeriya.
Sai dai yanzu haka kallo na shirin komawa kan makomar wadanda aka sako din na cewar ko ya ya ake ganin sakin nasu bayan sun dawo cikin al’umma, kasancewar tun da fari an killace su ne sakamakon wasu laifuka da suke aikatawa.
A dai ‘yan kwanakin da suka gabata ne jami’an ‘yan sanda suka samu nasarar kubutar da wasu da ke gidan marin a jihohin Kaduna da garin Daura na jihar Katsina.
Haka ma a nan Kano inda aka ruwaito cewa, wata makaranta ta ‘yan mari ta saki mutane 100 bisa radin kanta, inda wasu ke cewa hakan na da alaka da yadda ‘yan sanda suka rika kubutar da tsararrun.
Masana da dama dai na cewa, kamata ya yi a yi kokarin tsaftace harkar tafiyar da gidajen gyaran tarbiyyar maimakon rika sako ‘yan marin suna fantsama cikin jama’a.