Labarai
Koma wa yin jarrabawar WAEC da NECO a Kwamfuta ba zai hana satar jarrabawa ba- NUT

Kungiyar malaman makaranta ta Najeriya NUT, ta ce sauya tsarin gudanar da jarrabawar kammala makarantun sakandare ta WAEC da NECO zuwa tsarin amfani da Kwamfuta da za a aiwatar, ba zai kawo karshen satar jarrabawa ba.
Shugaban kungiyar na kasa Audu Amba, ne ya bayyana hakan a tattaunawar sa da manema labarai a birnin tarayya Abuja.
A kwanakin baya ne dai ministan ilimi Tunji Alausa ya sanar da matakin gwamnatin tarayya na canja tsarin jarabawar WAEC da NECO zuwa yinsu ta kwamfiyuta, wanda ya ce hakan zai kara ingantawa tare da rage satar amsar da dalibai keyi a lokacin jarrabawa.
You must be logged in to post a comment Login