Kasuwanci
Koriya ta bawa Najeriya dala miliyan 13 don shirin gudanar da gwamnati ta kafar Internet
Jamhuriyar Koriya ta sanya hannu a sabuwar yarjejeniyar aikin fadada shirin gudanar da gwamnati ta kafar Internet da zai lakume sama da dala miliyan 13 da Najeriya.
A shekarun baya Jamhuriyar ta Koriya dake yankin Asiya ta bayar da gudunmowa ga ayyukan gudanar da gwamnati ta kafar Internet a shekarar 2013 da 2019.
Ministan sadarwa da bunkasa tattalin arziki na kasa, Isa Ali Pantami da kuma Daraktan Hukumar Hadin Kan Kasa da Kasa ta Koriya, Woochan Chang suka sanya hannu a yarjejeniyar don kaddamar da kashi na biyu na aikin wanda zai gudana har zuwa shekarar 2026.
Ana sa ran aikin zai haɓaka ƙarfin ci gaba da aiwatar da muhimman tsare-tsaren babban shirin tafikar da gwamnati ta kafar Internet na ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login