Kiwon Lafiya
Kotu a jihar Kwara ta yi barazanar aikewa da babban sufeton ‘yansanda Ibrahim Idris gidan yari
Wata babbar kotun jihar Kwara da ke da zama a garin Ilorin babban birnin jihar karkashin jagorancin mai shari’a Ibrahim Yusuf, ta yi barazanar aikawa da sufeto janar na ‘yansandan kasar nan Ibrahim Idris gidan yari matukar ya ci gaba da raina umarnin kotu.
Kotun dai ta zargi Ibrahim Idris da kin bin umarnin da ta bashi na sakin mai taimakawa gwamnan jihar Kwara na musamman kan harkokin siyasa Olalekan Alabi.
Haka zalika kotun dai ta aikawa sufeto janar na ‘yansandan takardar barazanar ta cikin wani kundi mai dauke da sa hannun magatakardar kotun.
Cikin kundin, kotun ta gargadi Ibrahim Idris da cewa ko dai ya bi umarnin da ta bashi a ranar daya ga watan da muke ciki na Agusta ko kuma ya fuskanci fushinta.
Rundunar ‘yansandan kasar nan dai ta kama Olalekan Alabi a ranar Talatin ga watan Mayu sakamakon zargin sa da hannu cikin fashi da makami da aka yi a wasu bankuna a garin Offa da ke jihar ta Kwara.