Labarai
Kotu: A tilastawa tsohon mijina daukar dawainiyar ‘ya’yansa – Huraira Ali
Babbar kotun shari’ar musulinci dake Kofar Kudu karkashin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ta fara sauraron karar wata mata da ta nemi kotu ta tilastawa tsohon mijinta cigaba da daukar dawainiyar ‘ya’yansa tara da kuma basu wajen zama.
Tunda farko wadda ta shigar da kara Huraira Ali ta ce sun kwashe tsawon shekaru ashirin da mijinta Sharif Abubakar wanda a suka rabu shekara daya data wuce amma baya daukar nauyin ciyarda ‘ya’yansa da kuma wajen da za su zauna.
A cewar tsohon mujin nata Sharif Abubakar Panshekara bayan an bayyana masa hakkokin da ake zarginsa da gaza cikawa akan ‘ya’yansa, ya ce, sunje gurare da yawa domin samar musu da masalaha tsakaninsu amma sun gaza kaiwa ga ci.
A yayin zaman Kotun na yau Alhamis 11 ga watan Maris bayan kotu ta karantowa wanda ake kara Sharif Panshekara, ya ce, “Akan batun kudin ciyarwa ni dan fansho ne kuma naira dubu arba’in na ke samu a kowa ne wata kuma akwai ‘ya’ya na guda biyu a makarantar kwana kuma ni ke dawainiya dasu.”
Sai dai koda Kotu ta waiwayi Sharif domin jin ko nawa zai rika basu a wata, sai ya ce zai rika basu naira dubu goma sha biyar sannan kuma zai nema musu inda zasu zauna domin su cigaba da rayuwa.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito cewa mai shari’a Sarki Yola ya sanya ranar ashirin ga watan biyar domin yanke hukunci na karshe a shari’ar.
You must be logged in to post a comment Login