Labarai
Kotu ta aike da Mubarak Uniquepikin gidan yari bayan sukar Ganduje a Comedy
Kotun Majistiri mai lamba 58 da ke Nomansland a Kano ta aike da wasu matasa masu wasan barkwanci zuwa gidan yari.
An gurfanar da matasan ƴan wasan Barkwancin Mubarak Muhammad da aka fi sani da Uniquepikin da mai ja masa baƙi Nazifi Isah Muhammad a gaban Kotun bisa zarge-zarge guda huɗu.
Hukumar tace fina-finai ta Kano ce ta yi ƙararsu bisa zargin haɗa kai, da ɓata suna da cin zarafin Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje tare da yunƙurin tayar da hayaniya a wani faifan bidiyo da suka fitar.
Yayin zaman Kotun na yau Laraba waɗanda ake zargin sun amsa tuhumar da ake musu.
Lauyan da ke kare su da iyayensu, sun roƙi kotu da ta yi musu afuwa.
A nan ne kuma alƙalin Kotun mai shari’a Aminu Gabari ya ɗage shari’ar zuwa ranar Litinin 7 ga watan Nuwamban da muke ciki.
You must be logged in to post a comment Login