Kiwon Lafiya
Kotu: ta bada belin tsohon gwamnan jihar Ekiti kan kudi naira miliyan 50
Babbar Kotun tarayya ta Jihar Lagos karkashin mai Shari’a Mujisola Olatoregun ta ba da belin tsohon gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose kan kudi Naira Miliyan 50 a yau.
Haka zalika mai Shari’a Mujisola Olatoregun ta sanya sharadin mutanen biyun da za su tsaya ma sa dole su bayar da shaidar biyan harajin shekaru 3, baya ga wadancan kudade Naira miliyan 50.
Sannan ta bukaci Ayodele Fayose ya mikawa kotun Fasfonsa na tafiye-tafiye.
Tun da fari Lauyan Fayose Kanu Agabi ya nemi Kotun ta ba da belin tsohon gwamnan na Ekiti, kasancewar bisa radin kasa ya mika wuya ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC baya ga kasancewarsa mutum mai mutunci.
Sai dai EFCCn ta nuna rashin amincewarta da ba da belin bayan da ta ce Fayose ya samu rakiyar wasu fusatattun ‘yan bangar siyasa zuwa ofishinta, da ke da muradin farwa hukumar.
Kuma har yanzu hukumar na ci gaba da zakulo irin kadarorin da ya mallaka ta hanyar halasta kudaden haram.
Tsohon gwamnan na Ekiti na fuskantar tuhume-tuhume guda 11 da suka danganci halasta kudaden haram da suka kai Naira biliyan daya da miliyan 200, baya ga karbar kudi Naira biliyan daya da miliyan 200 ta haramtacciyar hanya don gudanar da yakin menan zabensa a shekar 2014.