Labarai
Kotu ta bayar da belin tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami SAN

Wata Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar da belin wucin gadi ga tsohon Ministan shari’a Abubakar Malami SAN, a shari’ar da Hukumar EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotu.
Alkalin kotun Mai shari’a Bello Kawu ne ya bayar da belin nasa bayan da ya saurari ƙarar da aka shigar a gaban kotun, inda ya amince da bayar da belin bisa wasu sharuɗɗa da suka hada da mika fasfo din tafiye-tafiyen Abubakar Malami, da kuma ɗaukar lamuni ta hannun masu tsaya masa mutum biyu.
Alkalin ya bayyana cewa, Masu tsaya masa za su kasance, babban Darakta a Hukumar Tallafin Shari’a ta kasa da kuma ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Augie da Argungu.
Mai shari’a Bello Kawu ya kuma ɗage sauraron shari’ar zuwa wani lokacin domin ci gaba da sauraron ƙarar, inda aka tabbatar da cewa Abubakar Malami ya amince da dukkan sharuɗɗan da aka gindaya masa.
You must be logged in to post a comment Login