Labarai
Kotu ta dage sauraran karar Abba Kabir kan zargin Ganduje da saida kadarorin gwamnati
Babbar kotu a jihar Kano ta dage ci gaba da saurarar karar da dan takarar gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya shigar ya na kalubalantar gwamnan Kano Abdullaji Umar Ganduje kan sayar da wasu daga cikin kadarorin gwamnati.
Wakilin mu Yusuf Nadabo Isam’il ya ruwaito cewa ,a yayin zaman kotun na yau, mai shari’a Nura Sagir ya dage saurar karar, har zuwa ranar 29 ga watan Oktobar shekarar da muke ciki.
Lauyan Abba Kabir Yusuf, wato Bashir Yusuf Tudun Wuzirici ya ce matakin da gwamnan jihar Kano ya dauka na saida kadarorin gwamnatin ya sabawa dokar tasarafi da filaye ta jihar Kano.
Ya yin da lauyan gwamnatin Kwmishinan shari’ar Barrista Musa Abdullahi Lawal ya ce korafin bashi da tushe ballantana makama.
Muna dauke da cikakken labarin a nan gaba
You must be logged in to post a comment Login