Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta dakatar da Ganduje daga shugabancin APC

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 4 karkashin jagorancin mai sharia Usman Na abba ta dakatar da shugaban jam’iyyar APC na kasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje daga bayyana kansa a matsayin shugaban jam iyyar har zuwa sanda za a kammala shari’a tsakaninsa da shugabannin jam iyyar na mazabar Ganduje.

Tun da fari wani mutum mai suna Haladu Gwanjo da ya bayyana kansa a matsayin mai bada shawara akan harkokin sharia na jam iyyar APC a mazabar Ganduje ne ya roki kotun da ta dakatar da Gandujen daga shugabancin jam iyyar da har zuwa sanda za a kammala jin korafinsu.

Kotun ta aminta da rokon inda aka ayyana cewar kada Ganduje ya sake bayyana kansa a matsayin shugaban jam iyyar har zuwa lokacin sauraron shari,ar hakan dai na faruwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin kano ta ke yunkurin gurfanar da Ganduje da mai dakinsa da dansa a gaban kotu a kan zargin rashawa.

 

Rahoton: Yusuf Nadabo Isma’il

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!