Labarai
Kotu ta fara sauraron karar kalubalantar nadin sabon Sarkin Zazzau
Babban kotun jihar Kaduna mai daraja ta daya karkashin jagorancin mai sharia Kabir Dabo ta fara sauraron karar da aka shigar gabanta na kalubalantar nadin da gwamnan jihar Kaduna Mal Nasir El-Rufa´i ya yi wa Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau.
An nada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau na goma sha tara biyo bayan rasuwan marigayi sarkin Zazzau Dr. Shehu Idris.
Wakilin mu Hassan Ibrahim ya rawaito cewa Babban Kotun ta jihar Kaduna karkashin jagoranchin justice Kabiru Dabo ya sanya ranar ashirin da bakwai ga wannan wata da muke ciki domin cigaba da sauraron karar bangarorin biyu bayan umarnin da kotu ta bayar na mika takardar ga wanda ake zargi wato bangaren gwamnatin jihar Kaduna,da kwamishinan kananan hukumomi da masarautu da masarautar zazzau,da masu zaben sarki da kuma sabon sarkin.
Alhaji Bashar Aminu Iyan Zazzau shi ne ya shigar da kara inda yake kalubalantar gwamnatin jihar Kaduna bisa wannan nadi da aka yi.
Yana mai cewa, yana neman kotun tabi tsarin da aka sani tun asali wajen zaben sarki a masarautar Zazzau.
You must be logged in to post a comment Login