Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta fara sauraron karar kalubalantar nadin sabon Sarkin Zazzau

Published

on

Babban kotun jihar Kaduna mai daraja ta daya  karkashin jagorancin mai sharia Kabir Dabo ta fara sauraron karar da aka shigar gabanta na kalubalantar nadin da gwamnan jihar Kaduna Mal Nasir El-Rufa´i ya yi wa Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau.

An nada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau na goma sha tara biyo bayan rasuwan marigayi sarkin Zazzau Dr. Shehu Idris.

Wakilin mu Hassan Ibrahim ya rawaito cewa Babban Kotun ta jihar Kaduna karkashin jagoranchin justice Kabiru Dabo ya sanya ranar ashirin da bakwai ga wannan wata da muke ciki domin cigaba  da sauraron karar bangarorin biyu bayan umarnin da kotu ta bayar na mika takardar ga wanda ake zargi   wato bangaren gwamnatin jihar Kaduna,da kwamishinan kananan hukumomi da masarautu da masarautar zazzau,da masu zaben sarki da kuma sabon sarkin.

Alhaji Bashar Aminu Iyan Zazzau shi ne ya shigar da kara inda yake kalubalantar gwamnatin jihar Kaduna bisa wannan nadi da aka yi.

Yana mai cewa, yana neman kotun tabi tsarin da aka sani tun asali wajen zaben sarki a masarautar Zazzau.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!