Labaran Kano
Kotu ta hana bada wayar malamin da ake zargin haike wa dalibarsa.
Kotun Majistret da ke unguwar Rijiyar Zaki a nan Kano, karkashin jagorancin mai sharia Aminu Usman Fagge, ta baiwa jamian yan sanda umarnin baiwa malamin nan da ake zargi da yunkurin yin lalata da dalibarsa kuma matar Aure mota da kuma katin shaidar aikinsa.
An dai gurfanar da malamin ne mai suna Dr. Masaudu Abdullahi wanda ke koyarwa a kwalejin aikin lafiya da ke garin Bebeji bayan da aka kama shi ya je gidan dalibar ta sa da niyyar aikata badala da ita.
A zaman kotun na jiya Talata dai lauyoyin malamin sun mika wa kotun bukatu 3 da suka hadar da neman baiwa malamin wayarsa ta hannu da mota da kuma katin shaidarsa.
Sai dai kotun ta ki amincewa da bukatar lauyoyin nasa na bashi wayarsa ta hannu inda kotun ta ce akwai hujjoji a cikin wayar na kalaman soyayya da ya rika aike wa dalibar tasa.