Labarai
Kotu ta hana Yan sanda rushe shagunan Bompai
Wata babbar kotu a Kano ta umurci rundunar ‘yan sanda da ta dakatar da shirin rushewar ko kutse ga shagunan da ke jikin bariki su da ke kan titin Independence, a yankin unguwar Bompai.
Alkalin kotun mai shari’a Aisha Ibrahim Mahmoud ce ta bayar da umarnin ta na mai dakatar da rundunar ‘yan sandan da cewa su dakata har sai ta kammala nazari a kan kararsu da wasu mutane suka shigar kan shagunan.
Wadanda suka shigar da karar su ne George Bassey da Kenneth K. Nliam da Joseph M. Yunusa da Haris Idris Idris da Sadik Umar Ado da Ifeanin Iheanacho a madadin kungiyar Bompai Multi-Purpose Cooperative Society.
Wadanda ake kara kuma sun hada da Sufeto Janar na rundunar yan sanda da mataimakin Sufeton ƴan sanda na shiyya ta daya da kuma Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano, sai O.C Works Zone 1 Kano da O.C Works.
Kotun ta ce ta bayar da umarnin na wucin gadi ne bayan sauraron karar da Lauyan masu kara Barista Sani Idris.
Haka kuma, kotun ta daga sauraron shari’ar zuwa ranar 30 ga watan nan da muke ciki na Janairu.
You must be logged in to post a comment Login