Labarai
Kotu ta haramta amfani da dokar kasafin kudin Rivers na Bana
Babbar kotu a Abuja ta soke kasafin kuɗin jihar Rivers na kimanin Naira Biliyan Dari Takwas wanda majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin ɓangaren Edison Ehie ta amince da shi kuma gwamna Siminalayi Fubara, ya sanya masa hannu.
Kotun ta yi hakan ne bayan da ta tabbatar da ƙarar da majalisar da shugabanta Martin Amaewhule suka shigar don kalubalantar Fubara da suka nemi a dakatar da gwamnan daga yi wa ayyukan majalisar a karkashin jagorancinsa makarkashiya.
BBC ta ruwaaito cewa, Ken Njemanze wanda lauyan Amaewhule ne ya zargi gwamnan da yin katsalandan ga ayyukan yan majalisa saɓanin yadda doka ta bambance ayyukansu.
Wanda ya shigar da karar ya nemi kotu ta hana wanda ake kara daga hana majalisar kudaden da take bukata na tafiyar da ayyukanta har da biyan albashi da alawus-alawus.
Da farko alkali James Omotosho ya ce Ehie ta hannun lauyansa Oluwole Aladedoye ya ce ya yi murabus daga majalisar dokokin jihar ta Rivers.
Omotosho ya ce Ehie ba shi da ikon shigar da kara saboda ba shi ne shugaban majalisar dokokin Ribas ba sannan kuma ba dan majalisa ba ne.
Idan za a iya tunawa, a ranar 13 ga watan Disamba, lokacin da rikicin siyasa ya yi zafi a jihar mai arzikin man fetur har ta kai ga rushe ginin majalisar, Fubara ya gabatar da kasafin na bana na kimanin wannan kudi gaban yan majalisa biyar karkashin Edison Ehie.
Gwamnan ya gabatar da kasafin kudin a fadar gwamnati da ke Fatakwal sakamakon rushe ginin majalisar da gwamnatin jihar ta yi sannan bayan kotu ta hana abokin hamayyar Ehie, Martins Amaewhule daga amfani da harabar majalisar.
You must be logged in to post a comment Login